Barka da warhaka,
Muna matukar farin sanar da maziyarta da mammbobin wannan gidan yana cewa dukkan mai bukatar wata waka ko yake da korafi to ya makala shi a sashin da ya dace a dandalin wannan gidan yana. Haka kuma daga yau ba zamu sake amsa email na bukatar wata waka ko kuma korafi ba matukar ba a dandali aka rubuta shi ba.
A gefe daya kuma, muna sake kira ga maziyarta da mambobin wannan gidan yana da cewa idan suna da wata waka (ban da wakokin fina-finan Hausa) ko kuma hoton wani/wata mawaki/ya da ya daure ya aiko mana wannan gidan yana domin amfanin dukkan al’umma.
Muna mai yi muku albishirin cewa Gangaran kuma Shaihun Malamin nan na tsangayar ilimi ta Bayero da ke Kano wato Farfesa Abdalla Uba Adamu zai bakuncemu nan bada dadewa ba.
Mun Gode
Sarkin Gidan Mawakan Hausa